Pezeshkian: Manufar Gwamnati Ita Ce Raya Dukkan Kasa

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna aiki fiye da ra’ayin siyasa don biyan buƙatun al’ummar kasa Shugaban kasar Iran ya yi kira kan kokarin

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna aiki fiye da ra’ayin siyasa don biyan buƙatun al’ummar kasa

Shugaban kasar Iran ya yi kira kan kokarin magance matsalolin tattalin arziki da rayuwa a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai.

Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ya ruwaito cewa: Shugaba kasar Iran Mas’oud Pezeshkian, a wani biki na Ziyara da kuma girmama iyalan shahidan gwamnati a lokuta daban-daban, wanda aka gudanar a Cibiyar Al’adu da Tarihi ta Sa’ad-abad, ya girmama ruhin wanda ya kafa juyin juya halin Musulunci tare da tunawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci da sauran shahidai da kuma shahadan Larijani, Nasir-zadeh, Hujaul-Islam Khatib da sauran shahidan juyin juya halin Musulunci, kuma ya bayyana cewa: Shahadan ministoci, kwamandojin soji da talakawa babban hasara ne da barna da masu ikirarin kare hakkin dan adam da dimokuradiyya suka yi wa kasar.

Shugaban ya soki dabi’ar yaudarar masu ikirarin kare hakkin dan adam, kuma ya lura cewa: Sun dade suna kiran Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin ‘yan ta’adda kuma mai tallafawa ‘yan ta’adda tsawon shekaru, amma tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, sun kashe jami’an Iran, kwamandoji da masana kimiyya a lukuta daban-daban.

Iran

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted