Al-Adu da ci gaban musulunci a tarihi 13

13-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, shi wanda

13-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, shi wanda yake kawo maku, irin ci gaban da musulmi suka samu a tsawon tarihin bayyanarsa. Wanda ni tahir amin nake kawo maku sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasnace tare da mu.

///…Idan masu sauraro suna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun yi Magana dangane da yanda ilmin likitanci taurari da sauransu suka kaura daga kasar Iran zuwa kasashen Larabawa.

Kafin haka mun bayyana cewa karnuka kimani 4 bayan bayyanar annabi Isa (a) kasar Farisa ta lokacin ta tarjami wadannan ilmomi daga kasashen girka. Kuma sun kafa makarantu a yankin Shushtar na kudancin kasar ta Farisa.  

Mun bayyana cewa, da farko musulmi sun fara da karfafa karatun al-kur’ani mai girma wanda shi ne asasin addinin musulunci, don haka da farko sai sun karfafa karatun al-kur’ani mai girma sannan su fara sauran karatu na fadada ilminsu a ko wani fanni yake.

Sannan mun yi maganar cewa an fara tarjamar littafai daban daban daga harsunan girka, farisanci da indiyanci zuwa harshen larabci tun tsakiyar karni na biyu har zuwa karni na hudu hijiriyya. Kuma kafin haka an tarjama mafi yawan littafan da ake bukata don tafiyar da makarantu da kuma jami’o’ii a dukkan daular musulunci.

Banda haka mun bayyana cewa a tsakanin karshen sarakunan banu umayya da kuma farkon sarakunan Abbasiyawa, Imam jaafar dan Muhammad Assadik limami na shiga daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), ya yada ilmi mai yawa na sanin All..ko addini da kuma sauran ilmomi na zamani, wadanda suka hada da na likitanci, kimiyyar sinadarai, ilmin jayayya ko muhawaran ilmi, da saurasnu.

Imam Sadik (a) yana da dalibai kimani 4000 daga cikin mabiyansa ko shi’arsa da sauran musulmi. Mafi yawansu a fagen addinin. Ya koyawa Jabir dan Hanyan ilmin kimiyar sinadarai, kuma shi ne ya samar da sinadarin sulfuric Acid a karon farko

A zamanin banu Umayya an tarjama littafai da dama daga harshen girka zuwa harshen larabci, daya daga cikin littafan da aka tarjama akwai littafin Konnash wanda Masrujuwwiyya ya rubuta a zamanin Marwan na farko,  kuma manufarsa na tarjama wannan littafin shi ne saboda koyon harkokin siyasa da kasuwanci, kuma yadda za’a yi hulda da yan kasar waje wadanda ba larabawa ba.

Sai dai tarjama ta babba wacce ta shafi dukkan bangarorin ilmi an yisu ne a zamanin sarakunan Abbasiyawa, wannan tarjamar ta yi tasiri sosai a cikin al-ummar musulmi. Wadan nan ayyukan tarjama sun dau kimani shekaru 200 ana yinsa, kuma sarki Mansur Dawaniki sarki na biyu daga sarakunan Abbasiyawa, shi ne ya assada aikin tarjama mafi girma a cikin tarihin musulunci, wasu malaman tarihi sun bayyana cewa sarki Mansur ne ya gina ayyukan tarjama a cikin al-ummar musulmi.

Sarki Mansur ne ya maida birnin Bagdaza a matsayin babban birnin daular Musulunci a lokacin.

Sarki Mansur ya jawo masana taurari zuwa fadarsa, suna masa aiki dare da rana, kuma baya yin wani abu mai muhimmanci sai ya tambaesu, don yayi aikinsa cikin shawarar da malaman taurari suka bashi. Sannan sauran sarakuna karkashin daularsa suka dauka daga gareshi.

Malaman taurari Iraniyawa a lokacin sun fi korewa a wannan fannin ne, don haka ya dogara da su don yin wannan aikin. Sai dai me al-kur’ani mai girma take daukar malaman taurari? Shin ya halatta musulmi su dogara dailmin taurari don sanin lokutan sallah, azumi, hajji da Al-gibla haramcin yaki a cikin watannin masu al-farma, yin tunani a cikin al-amuran sammai da kassai da sauransu? Wasu malamai suna ganin ba laifi.

 Don haka mafi shahara a sanin ilmin taurari a lokacin suna yan gidan Nubkati, wadanda bayan shigarsu addinin musulunci, daga baya sun shiga marhabar shi’a. Wadan nan Iraniyawa sun dade a fadojin sarakunan Abbasiyawa a lokacin, inda suke masu aikin tarjama da lissafin taurari da lokutan dare da rana a garesu a duk tsawon shekara.

Nubhakht da dansa Abu-Sahal dan Nubakht sun tarjama wasu littafai dangane da tafiyar taurari da kuma amfaninsu ga musulmi a lokacin.

Banda bayyana ra’ayinsu kan littafan da suka tarjama, baban Mohammad dan Ibrahim Fazari, wato babansa ne mutum na farko wanda ya gina na’urar lissafin tafiyar taurari a cikin musulmi. A cikin wani littafinsa mai suna Sinaad Hind babba, wanda aka ci gaba da Amfani da shi har zuwa zamanin sarki Mamun dan sarki Haruna Rashid, ya koyawa musul miilmin taurari masu yawa kuma a cikinsa ne suka koyi lissafi da haruffan indiyanci. Don haka larabawa suna irge ne da irin irgen indiyawa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted