Iran Tana Da Hanyoyin Kare Kanta Daga Takunkumin Amurka

Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Suna da tsarin tunkarar kowane irin mummunan manufa kan kasar Iran Kakakin Rundunar

Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Suna da tsarin tunkarar kowane irin mummunan manufa kan kasar Iran

Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC), Janar Hossein Mohebi, ya yi ikirarin cewa: Suna da wani yanayi da za su iya magance tasirin yakin tattalin arziki da abokan gaba suka kakaba kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Da yake magana game da yakin tattalin arziki, Janar Mohebi ya ci gaba da bayyana cewa: Shugaban Amurka Donald Trump yanzu ya yarda ya ba da umarnin yakin tattalin arziki kan Iran, kuma an riga an sanya wa Iran takunkumi mafi tsauri. Ya kara da cewa, “Idan aka duba a hankali, wannan amincewa na iya nufin amincewa da shan kaye a fagen soja, domin da sun yi nasara a fannin soja, da ba za a bukaci a koma ga yakin tattalin arziki ba.”

Ya kuma kara da cewa: “A gefe guda kuma, yakin tattalin arziki ba sabon abu bane. Iran ta shafe tsawon shekaru 47 tana fuskantar yakin tattalin arziki da takunkumai.” Ya bayyana cewa sun sha sanar da cewa suna da yanayi ga kowane aiki na abokan gaba, kuma an tsara wasu yanayi don kawar da tasirin matakan tattalin arziki mara kyau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted