Isra’ila Ta Razana Da Shawarar Da Aka Gabatawa Iran Ta Shiga Yarjejeniyar Makka

Jaridar "Haaratz" ta Isra'ila ta nakalto shugabar cibiyar Nazari "Mitifim" Kisniya Sabtolva tana cewa; Idan har Iran ta shiga cikin wannan yarjejeniyar, to hakan zai
Yarjejeniyar Makka

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambato majiyar majalisar shawarar musulunci ta Iran tana cewa, an kaddamar wa da kasar shawarar shiga cikin yarjejeniyar Makkah.

Tashar talabijin din ta “almayadin” ta ambato Mahdi Rahimi wanda shi ne shugaban kamfanin dillancin labarum watsa labaru na majalisar shawarar yana cewa; shawarar da aka gabatarwa Iran akan shiga cikin wannan yarjejeniyar ya tayar wa da Isra’ila hankali.

Jaridar “Haaratz” ta Isra’ila ta nakalto shugabar cibiyar Nazari “Mitifim” Kisniya Sabtolva tana cewa; Idan har Iran ta shiga cikin wannan yarjejeniyar, to hakan zai samar da gagarumin sauyi.”

Bugu da kari, ta ce; Shigar Iran cikin wannan yarjejeniyar zai kara zubar da mutuncin Amurka, domin ba za su ji dadin kawance irin wannan ba, haka nan Isra’ila da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

Tun da fari kasashen Saudiyya, Turkiya da Pakistan sun sanar da cewa kawancen nasu ba su yi shi domin fuskantar Iran ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted