Tsohon shugaban kasar Bolivia Morales ya jinjinawa Iran tare da bayyana ta a matsayin kyakkyawan misali na kare mutuncin al’ummarta wajen kalubalantar Daular Danniya
Tsohon shugaban kasar ta Bolivia Evo Morales ya rubuta hakan ne a shafinsa na X sannan ya kara da cewa: ” Ci gaban zamani da Iran take da shi ta fuskar kere-kere ya ba ta damar rage tazarar da take a tsakaninta da Amurka ta fuskar soja.”
Haka nan kuma tsohon shugaban kasar ta Bolivia ya ce; Al’ummar Iran sun fuskanci yakin da aka shelanta musu ta hanyar hadin kai, haka nan kuma fuskantar matsin lamba na tattalin arziki da Amurkan ta shekanta akansu.”
Wani sashe na bayanin Evo Morales ya kunshi cewa; “Daular Danniya tana da karfi da za ta iya kafa takunkumai da shelanta yaki,amma ba za ta iya tilastawa al’umma yi ma ta biyayya ba.”
Evo Morales ta kuma ce; Iran ta tabbatar da cewa tana da karfin da za ta iya yin nasara a cikin yakin tattalin arziki da aka shelanta a kanta.”