Mai Magana da yawun dakarun kare juyin musulunci ya yi watsi da abinda Amurka ta riya na cewa, sun rusa na’urorin “Radar” na hango nesa, da Iran take da su, da hakan zai bayar da damar wucewar jiragen ruwa ta mashigar Hurmuz.
Kakakin dakarun kare juyin musuluncin na Iran Hussain Muhibbi ya ce, Abinda Amurkan suke riyawa kambami ne na watsa labaru.”
Muhibbi ya kuma ce; Kayan aikin da Iran take da su na hango kai da komowar makiya, ba Radar ba ce kadai.
Haka nan kuma ya ce; Hanyoyin hango nesa da Iran take da su, ba dole su zama tauraron dan’adam ba, kamar yadda Amurkawan suke zato, da akwai wasu hanyoyin da ba dole ne makiyan su iya gano ta ba.”
Muhibbi ya kuma ce; Idan har jamhuriyar musulunci ba ta da hanyoyin leko nesa, to ta yaya take iya kai hari ya kuma sauka daidai akan wurare masu muhimmanci na jiragen ruwa?.
Wani sashe na jawabin kakakin IRGC din ya kunshi bayani akan yadda Iran ta tsokane idanun makiya ta yadda ta lalata na’urorinsu na “Radar”.