Search
Close this search box.

‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Nasarar Rusa Majalisar Yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Jami’i a kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun yi nasarar wargaza majalisar yakin yahudawan sahayoniyya Wakilin ofishin siyasa na kungiyar

Jami’i a kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun yi nasarar wargaza majalisar yakin yahudawan sahayoniyya

Wakilin ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Izzat Al-Rishq ya bayyana cewa: ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa karkashin jagorancin dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas sun yi nasarar rusa majalisar yakin yahudawan sahayoniyya da aka kafa watanni 8 da suka gabata don kawo karshen ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, fira ministan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a jiya Litinin, a wani zama na ministocinsa kan tsaro da siyasa, matakinsa na rusa majalisar ministocin yaki bayan murabus din ministoci biyu, wato Benny Gantz da Gadi Eisenkot.

Kafar yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce: Netanyahu ya sanar da ministocin gwamnatinsa matakin rusa majalisar yakin haramtacciyar kasar Isra’ila bayan Itamar Ben Gvir ya bukaci shiga cikinta.

Tun bayan murabus din Gadi Eisenkot, Ministan Tsaron Kasa mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben Gvir ya bukaci shiga cikin majalisar yakin haramtacciyar kasar Isra’ila, lamarin da Netanyahu bai so hakan ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments