An Sami Gawar Mace Ta 10 Da Aka Kashe A Kasar Afirka Ta Kudu

Gano gawar wannan mace, ya sake samar da damuwa saboda yadda a baya aka sami irinta 9 da ba tare da har yanzu an tantance
shugaba Remaphosa

‘Yan sandan kasar Afirka ta kudu  sun sanar da gano gawar mace ta 10 da aka kashe a yankin Ekurhuleni.

Gano gawar wannan mace, ya sake samar da damuwa saboda yadda a baya aka sami irinta 9 da ba tare da har yanzu an tantance dalilan yin hakan ba, ko masu yinsa ba.

Kakakin ‘yan sanda Birgediya Muridili ya fada wa manema labaru cewa:

” Abinda za mu iya fada a wannan lokacin shi ne cewa; mu gano gawo, kuma dukkanin jami’an ‘yan sanda masu bincike suna wurin da aka aikata laifin suna gudanar da aiki.

Wani jami’in yan sanda a yankin Tommy Mthombeni ya ce; Da alama matar an kashe ta ne ta hanyar yi mata rajamu.

Sauran mata  9 da aka kashe, shekarunsu suna a tsakanin 20 zuwa 30 ne kuma duk sai da aka cire musu tufafi.

Mace ta farko da aka kashe shekarunta 37, an same ta ne a ranar 15 ga watan Yuli. A wancan lokacin an kama mutum daya da ake zargi, kwanaki biyu, bayan kisan.

Hukumar ‘yan sanda ta ware kudin da sun kai Dalar Amurka 25,000 ga duk wanda ya kawo labari akan masu wannan kisan. Ita ma jam’iyyar Democratic Alliance ta ware kudin da sun kai dala 31,000 ga wanda zai kawo labari.

Kasar Afirka ta kudu mai mutane miliyan 62 tana cikin kasashen da aka fi kashe mutane a duniya,domin a kowace rana ana kashe abinda ya kai mutane 60.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted