A shirin tsaron kasar Iran daga makiya, da kuma makon karikai a jiya Jumma’a ce aka gudanar da jerin gwanon mahaya Babura 40,000 a nann birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa masu sa kai kimani 40,000 ne suka gudanar da jerin gwano na Babura daga dandalin Imam Hussain(a) a tsakiyar Birnin Tehran zuwa dandalin Azadi.
Gwamnatin kasar Iran tana son samar da jami’an tsaro masu sa kai wadanda kuma zasu kare kasar daga makiya har 313,000.
A makon da ya gabata an gudanar da jerin gwano ma wato 18 ga watan satumba an gudanar da irin wannan jerin gwanon inda dubban daruruwan masu sa kai suka gudanar da jerin gwano don nuna karfi da kuma shirin fuskantar duk wani makiyin da ya yi kokarin shiga kasar Iran.
Tun bayan da Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yaki a ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekarar , suka kuma kasa samun nasarar kifar da JMI suka fara barazanar zasu mamaye kasar.
Anan ne gwamnatin kasar ta bude rigistan tara mayaka masu su kai inda ta samu mutum miliyon 30 suka yi rijistan sunayensu.