Ofishin Fira ministan kasar Iraki Ali al-Zaydi ya sanar da cewa a halin yanzu suna tattaunawa da Amurka domin yin togiya ga wasu filayen saukar jiragen saman kasar daga takunkumin da Amurkan ta kakabawa jiragen saman Iran saboda su rika sauka a can.
Ofishin Fira ministan na Iraki ya ce, fagagen da suke yin a yi togiya akansu da akwai na ayyukan agaji, magani da kuma karatu.
A yau Asabar ne dai ofishin Fira ministan na kasar Iraki ya fitar da wannan sanarwar tare da cewa kasarsa tana matukar kokarin ganin an sami dawowar zaman lafiya a cikin wannan yankin.
A kasar Iraki dai kungiyoyi da dama na farar hula da malaman addini suna sukar gwammatin kasar saboda matakin da ta dauka na aiki da takunkumin Amurka akan Iran.
A gefe daya, jakadan Iraki a Iran Yasir al-Hajjaj ya fada a yau Asabar cewa; rufewa jiragen Iran filayen jiragen sama da aka yi na wucin gadi ne, kuma gwamnatin kasarsa tana kokarin ganin an sake bude shi.
Jakadan na Iraki a Iran ya kuma ce; rufe filayen jiragen yana da tasiri maran kyau ga al’ummar Irakin, don haka sake bude shi ba zai tsaya a cikin kai da komowa saboda yawoin bude ido ba kadai.
Jiragen Iran dai suna ci gaba da zuwa kasashen duniya da dama da su ka hada China, Malysia da Turkiya. Haka nan kuma Pakistan.Vietmnem da Afghanistan.