Sanadiyyar hare-haren wuce gona da iri na sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila a Gaza an sami shahidi guda daya, yayin da wasu da dama su ka jikkata.
Majiyar Falasdinawa ta ce da safiyar yau Asabar cewa sanadiyyar harin haramtacciyar Kasar Isra’ilan da ta kai a yankin na zirin Gaza, da ya yi sanadiyyar shahadar wani matashi.
A yankin Khan-Yunus wasu Falasdinawa da dama sun jikkata saboda hare-haren na ‘yan Sahayoniya daga cikinsu da akwai karamar yarinya a sansanin ‘yan hijira na “almawasi”.
Kai hare-haren ‘yan sahayoniya akan yankin Falasdinawa a Gaza yana a karkashin keta yarjejeniyar tsagita wutar yaki ta shekarar da ta gabata.
Fiye da mutum 1000 ne sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kashe a wannan tsakanin, yayin da wasu dubbai su ka jikkata.