Wani dan kunar bakin wake ya kai hari akan wani wajen bincike na ‘yan sandan a yankin Khaybar da hakan ya yi sanadiyyar rushewar wurin baki da kuma daukar rayukan jami’an tsaro 11 da jikkata wasu.
Kafafen watsa labarun kasar ta Paksitan sun ce an kai harin ne akan iyakar kasar da Afghanistan a garin “Isma’il Dire Kha” wanda bayan cin rayukan mutane 11 ya kuma jikkata wasu 30.
Kasashen biyu dai suna fama da sabani bayan da Pakistan ta zargi Afghanistan da bayar da masu kai mata hare-hare mafaka,zargin da Kabul ta kore.