MDD Ta Yi Gargadin Cewa Ci Gaba Da Rufe Hurmuz Yana Barazana Ga Rayuwar Mutane Miliyan 45

Karamin sakataren  MDD mai kula da manyan ayyuka Jorge Moreira  Da Silver ya bayyana cewa; Za a iya kaucewa matsalar tsaron da mutum ne ya

ginin MDD

Karamin sakataren  MDD mai kula da manyan ayyuka Jorge Moreira  Da Silver ya bayyana cewa; Za a iya kaucewa matsalar tsaron da mutum ne ya kirkire ta wacce ta shafi mutane miliyan 45 da za a iya jefa su cikin matsanancin karancin abinci.

Jami’in na MDD ya kuma ce;Idan ace za a bar jiragen ruwa guda biyar masu dauke da takin zamani su wuce ta mahsigar Hurmuz a kowace rana, to abu ne mai yiyuwa a kaucewa fadawa cikin matsanancin yanayi na karancin abinci.

Jami’in na MDD ya kuma yi kira ga bangarorin da suke fada da juna da su samo mafita cikin gaggawa akan batun yadda takin zamani zai rika wucewa, nesa da batun tsagaita wuta da tattaunawa.

Haka nan kuma ya ce;

” Kasashe masu tasowa za su so ace suna da wadataccen abinci da ace sun fada cikin yanayi na neman taimako  da dogaro da kayan agaji.”

Kusan kasu 1/3 na takin zamanin da ake amfani da shi a duniya yana wucewa ne ta mashigar ruwar Hurmuz,kamar yadda MDD ta bayyana.

Iran dai ta dorawa Amurka alhakin abin yake faruwa na rashin tsaro a mashigar Ruwan Hurmuz saboda yakin da ta kallafa mata wanda bay a bisa doka.

Bugu da kari Iran ta sha jaddada cewa yanayin mashigar Ruwan na Hurmuz ba zai sake komawa kamar yadda yake a baya ba, gabanin shelanta yakin zalunci a kanta.

A hirar da tashar talabinin din Aljazeera ta yi da shugaban kasar Iran, ya bayyana cewa; Babu yadda za a iya bude mashigar Ruwan Hurmuz ta hanyar amfani karfi. Haka nan kuma ya ce; ta hanyar tattaunawa ne da diplomasiyya za a iya cimma matsayar da za ta kai ga bude wannan mashigar Ruwan mai muhimmanci ga duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted