Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana cewa; Ina yin yabo da jinjina ga shugaban kasar China Xi Jinping saboda zurfin tunaninsa da ya nuna goyon bayansa ga yarjejeniyar “Islamabad domin warware sabanin da ake da shi ta hanyar diplomasiyya.”
Shugaban na kasar Iran ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Juma’a, yana mai ci gaba da cewa; Iran tana goyon bayan aiki da wannan yarjejeniyar da abubuwan da ta kunsa da aka amince da su, da kuma samar da yanayin da ya dace domin akai ga bude tattaunawa ta gaske wacce za ta kai ga samar da sakamako.
Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya bayyana yadda Tehran da Beijing su ka yi tarayya akan kare hurumin kasashe da kuma kawo karshen rikici da dawo da zaman lafiya a cikin wannan yankin.
A yayin ganawar da shugaban kasar China Xi Jinping ya yi da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Washington a ranar Alhamis din da ta gabata, ya kira yi Amurkan da koma aiki da yarjejeniyar watan Yuni da Iran da kuma aiki da hanyoyin diplomasiyya da aka ayyana a karkashin wannan yarjejeniyar ta Islamabad.
Tun a ranar 16 ga watan Satumba da aka yi ganawa a tsakanin Ministan harkokin wajen China Wang Yi da takwaransa na Iran Abbas Arakchi, China din ta yi kira da a koma aiki da waccan yarjejeniyar ta fhaimtar juna.
A ranar 17 ga watan Yuni ne dai aka rattaba hannu akan yarjejeniyar fahimtar juna a tsakanin Iran da Amurka wacce ta kai ga tsayar da wutar yaki, bayan shiga tsakanin kasashen Pakistan da Qatar.
Sai dai Amurka ta ki yin aiki da sharuddan da su ka zo a cikin yarjejeniyar ta Pakistan, ta hanyar kawo hare-hare akan Iran, da Iran din ta rika mayar da martani mai tsanani akan sansanonin Amurka da sojojinta da suke a cikin kasashen larabawan yankin tekun pasha.