Sudan : Wani Rukunin Dakarun RSF, Ya Balle Zuwa Bangaren Sojoji

Sabon rukunin da ya balle, ya isa filin jirgin saman Khartoum tare da shiga aikin sojojin kasar.

A Soudan, wani rukuni daga rundinar kai daukin gaggawa ta RSF, ya balle ya koma bangaren sojojin Khartoum.

Shugaban rukunin ya nemi afuwar al’ummar da kuma Shugaban Majalisar Mulkin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan.

Kamfanin dillancin labarai na Sudan, SUNA, ya rawaito cewa sabon rukunin da ya balle, ya isa filin jirgin saman Khartoum tare da shiga aikin sojojin kasar.

A cewar SUNA, rukunin yana karkashin jagorancin Manjo Janar Ammar Mohammed Zein Rabih, wanda shi ne sakatare mai kula da yankin Darfur a kungiyar ‘Revolutionary Justice and Equality Movement’, kuma jami’i ne a cikin rundunonin da ke tallafawa RSF.

A ranar Litinin, Rabih ya shaida wa manema labarai a filin jirgin saman cewa, rukunin ya yanke shawarar “rabuwa gaba daya” da RSF, tare da yin yaki kafada da kafada da sojojin Sudan.

Ya ce, “An dauki wannan matakin ne saboda munanan ayyuka, kisan kiyashi, sace-sacen dukiyoyi, da kuma kashe fararen hula a jihohin Gezira, Khartoum, Darfur, da kuma birnin Al Fasher.”

Rabih ya kuma yi ikirarin cewa akwai kaburburan gama-gari da ke dauke da gawarwakin fararen hula da dama a kusa da filin jirgin saman Al Fasher, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su gudanar da bincike a wurin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted