Falasdinawa 6 Ne Suka Yi Shahada Wasu Suka Jikkata A Gaza

Falasdinawa shida ne suka yi shahada ciki har da yara biyu da mace daya a hare-haren da sojojin mamaya suke ci gaba da kai wa

Falasdinawa shida ne suka yi shahada ciki har da yara biyu da mace daya a hare-haren da sojojin mamaya suke ci gaba da kai wa kan Gaza

Falasdinawa shida, ciki har da yara biyu, sun yi shahada yayin da wasu suka jikkata a jerin hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a yankin Gaza a safiyar jiya Laraba. Hare-haren sun hada da hare-haren sama, bude wutan harsasai na manyan bindigogi da hare-haren jiragen sama marasa matuki gami da rushe-rushen gine-ginen gidaje, duk a cikin tsarin saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya ruwaito cewa: A arewacin Zirin Gaza, an kashe Hazem Majdi Muhammad Hamouda, mai shekaru 32, a lokacin wani harin sama da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani tanti da ke dauke da mutanen da suka rasa matsuguninsu a sansanin Halawa da ke Jabalia. Sannan an kashe wani Bafalasdine kuma wasu sun jikkata lokacin da wani jirgin sama mara matuki na sojojin mamayar Isra’ila ya kai hari kan sansanin Masar da mutanen da suka rasa matsuguninsu a yankin Tuam, arewa maso yammacin birnin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted