Amnesty International: Isra’ila Tana Hana Haihuwa A Gaza

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta nuna damuwarta kan yadda Isra’ila ke ƙoƙarin takaita haihuwa a Gaza Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta nuna damuwarta kan yadda Isra’ila ke ƙoƙarin takaita haihuwa a Gaza

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta zargi Isra’ila da ɗaukar matakan da suke raunana ƙarfin haihuwa a yankin Gaza, wanda hakan ke haifar da ƙaruwar zubar da ciki da hana haihuwar jarirai da kuma ƙara haɗarin lafiya ga mata masu juna biyu, uwaye da jarirai. Ƙungiyar ta yi gargaɗi game da mummunan sakamako ga lafiyar haihuwa a yankin.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Kungiyar Amnesty International ta bayyana a cikin wani rahoto da ta fitar kan hirarraki 228 cewa: Ayyukan Isra’ila sun haifar da damuwa sosai game da yuwuwar yin yunƙurin takaita haihuwa a Gaza.

Rahoton ya bayyana cewa: Dukkan asibitoci guda tara na IVF a yankin sun daina aiki, kuma lalacewar ta haifar da hasarar dubban tayi da ƙwai na haihuwa da ake adanawa, wanda hakan ya hana iyalan Falasɗinawa damar samun yara.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa: Takunkumin Isra’ila kan shigar da kayan agaji da magunguna ya ƙara ta’azzara haɗarin da mata masu juna biyu ke fuskanta da kuma ƙara yawan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.

Amnesty International ta yi kira ga Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya da ta binciki yiwuwar cewa: Jami’an Isra’ila sun aikata kisan kare dangi, kuma sun haɗa da lalacewar harkar lafiyar haihuwa a yankin Gaza a cikin iyakokin bincikenta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted