A Amurka ana ci gaba da caccakar Hukumar Kula Da Shige a Fice da Kwastom ta ICE, bayan cafke wasu mutane biyu da karfin tsiya a filin jirgin sama na Washigton.
Gwamnan Washigton ya ce Hukumar ta ICE Na “wuce gona da iri,” bayan kama wasu mutane biyu da aka yi a filin jirgin sama na Seattle-Tacoma.
“Muna bukatar tsarin tsaro na shige da fice da kan iyaka wanda ke da tasiri, da’a, da kuma mutuntaka.
ICE ba ta cika wadannan sharuddan ba, inji” Bob Ferguson, a cikin wani sako a kan shaffin X, bayan hotunan da ke nuna mutane biyu da aka kama a kan hanyar jirgin saman sun yadu a shafukan sada zumunta.
“Cin zarafin da aka yi a filin jirgin saman sun zama misali na baya-bayan nan na dabarun ICE,” in ji shi, yana kira da a soke hukumar.
ICE ta “wuce gona da iri,” a cewar gwamnan, ya kuma bayyana cewa ya “fusata, kamar sauran Amurkawa da yawa, ganin jami’an tsaro masu rufe fuska, suna jan mutane daga jiragen sama yayin da suke shiga jirgin.”