Jagoran juyin musulunci na kasar iran Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamena’I acikin sakon da ya aike da shi a makon dakarun sa kai na kasa wato Basij yace dakarun sa kai ba za su bar wata dama ba wajen kai hari kan makiya musulunci da kuma juyin musulunci na iran, haka zalika yayi kira ga dakarun da su fadada samuwarsu a fadin kasar , kuma su yi amfani da dukkan karfinsu wajen ciyar da iran gaba
Haka zalika jagoran ya kara da cewa kudurin kungiyar basij na bin koyarwa imam hussaini (As) shi ne ke jagorantar yadda take muamala da jama’a da kuma abokan gabarta, akwai koyarwar alkur’ani guda biyu masu kara karfin zuciya wato masu tausayi a tsakaninsu da kuma masu tsauri ga kafirai wadanda su ne haske masu haskaka zukatan mambobin kungiyar ta sa kai.
Iran na gudanar da bikin makon dakarun sa kai a duk shekara a karshen watan nuwamba domin tunawa da ranar kafa kungiyar dakarun sa kai ta Basij a ranar 26 ga watan nuwamban shekara ta 1979 sakamakon umarni da jagoran juyin musulunci na iran ya bayar a lokacin ayatollah ruhullah al khumaini.
Yace kungiyar basij ta fara nuna karfinta ne a lokacin yakin da aka kwashe shekaru 8 ana yi, inda kasancewarta ta zama mai tasiri a fagen daga kuma ta zama babban ginshiki tsaro a lokacin yakin.