Akraminia: Iran Tana Tsananta Sa-Ido A Mashigar Ruwan Hormuz

Kakakin Rundunar Sojin Iran ya jaddada cewa: Ana ƙarfafa iko da sa ido kan mashigar ruwan Hormuz Kakakin rundunar sojin kasar Iran Birgediya Janar Muhammad

Kakakin Rundunar Sojin Iran ya jaddada cewa: Ana ƙarfafa iko da sa ido kan mashigar ruwan Hormuz

Kakakin rundunar sojin kasar Iran Birgediya Janar Muhammad Akraminia ya tabbatar da cewa: Matakin shirye-shiryen rundunar ya karu idan aka kwatanta da na baya, kuma iko da sa ido kan mashigar Hormuz yanzu ya fi tsauri.

Akraminia ya bayyana cewa: Matakin sa ido kan mashigar Hormuz ya inganta tare da gabatar da sabbin tsare-tsare, sabunta tsarin da ake da shi, da kuma karfafa tsarin yaki na rundunar, yana mai jaddada cewa: Wannan hanyar za ta ci gaba da aiki sosai.

Dangane da halin da ake ciki a mashigar Hormuz, ya bayyana cewa: Wasu jiragen ruwa da suka ratsa wannan mashigar ruwa a cikin ‘yan makonnin nan ba tare da bada hadin gwiwa da sojojin ba sun fuskanci hari na nakiyoyin ruwa.

Kakakin rundunar ya bukaci masu jiragen ruwa da ke son ratsa mashigar Hormuz lafiya su hada kai da rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Birgediya Janar Akraminia ya kara da cewa gabatar da sabbin tsare-tsare, sabunta tsarin da ake da shi, da kuma karfafa tsarin yaki na rundunar sun taimaka wajen kara yawan sa ido kan mashigar Hormuz, yana mai jaddada cewa wannan tsari zai ci gaba da aiki sosai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted