Dubban daruruwan matasan Turai na zanga-zanga don neman kare makomarsu da kuma kin amincewa da yaki.
Tun daga ranar Juma’a an gudanar da irin wannan zanga zanga a biranen Berlin, Paris, Madrid, Milan, Vienna inda daruruwan dubban matasa suka bazu a tituna a kan manyan bukatu guda biyu: makomar matasa, da kuma tsadar rayuwa.
Suna masu kuma yin Allah wadai kan yadda gwamnatocin kasashensu ke fifita kasafin kudin soja, wanda suka ce yana zuwa ne ta hanyar rage kasafin ilimi, yaki da sauyin yanayi, kiwon lafiya da ayyukan gwamnati.
Bayanai sun ce bisa ga kiran kungiyar matasa, an gudanar da zanga-zanga a birane sama da 500 a fadin kasashe 27, a cewar alkaluman da kungiyar ta fitar wadanda kuma France24 ta ruwaito.
An ci gaba da zanga-zangar a duk tsawon karshen mako har zuwa ranar Litinin, musamman a Faransa, Belgium, Girka, Italiya, Portugal, da Burtaniya. Wannan matakin da aka tsara wani bangare ne na zanga-zangar da aka shafe makonni da dama ana yi a fadin Turai, musamman a Faransa.