Abbas Araqchi: Isra’ila Tana Ingiza Amurka Kan Yaki Da Iran

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Isra’ila tana zargin Iran da ƙera makamai masu guba don yaudarar Amurka da kuma tura ta zuwa yaƙi

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Isra’ila tana zargin Iran da ƙera makamai masu guba don yaudarar Amurka da kuma tura ta zuwa yaƙi a madadinta

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: “Ƙungiyar Yahudawan Sahayoniyya tana zargin Iran da ƙera makamai masu guba don yaudarar Amurka da kuma tura ta zuwa ga kunna wutar yaƙi a madadinta.”

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr, Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana manufar ƙungiyar Yahudawan Sahayoniyya da ke yada wannan fitina ita ce neman yaɗa iƙirarin ƙarya a kan Iran domin data zaune tsaye.

Araqchi ya nuna cewa: “ƙungiyar Yahudawan Sahayoniyya ta ƙi shiga kowace yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa da ta hana kera makaman nukiliya, sinadarai masu guba ko na halittu. Wannan ƙungiyar tana da ɗaruruwan makaman nukiliya, ta kai hari kan ƙasashe bakwai a yankin, kuma ta mamaye wasu sassan ƙasashen uku. Bugu da ƙari, a cikin shekarar da ta gabata kaɗai, ta jawo Amurka cikin yaƙe-yaƙe biyu da suka gaza a kan Iran.”

Ya ƙara da cewa: “Yanzu, wannan ƙungiyar mai tayar da hankali tana ƙara zarge-zarge a kan Iran, ƙasa mamba a Yarjejeniyar hana yaɗuwar Makamai Masu Guba (NPT) da kuma Ƙungiyar Haramta Makamai Masu Guba (OPCW), wadda ita kanta ta kasance wacce aka zalunta da makaman guba da Jamus ta Yamma ta bai wa gwamnatin Saddam Hussein. Wannan ƙungiyar tana da’awar cewa Iran tana samarwa da ɓoye irin waɗannan muggan makamai a cikin masana’antun magunguna!”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted