Iran Ta Yi Gargadi Kan Amfani Da AI Don Manufar Soja

"Dole ne fasaha ta yi wa dan adam hidima'' inji wakilin Iran a MDD.

Iran, ta yi gargadi akan amfani da kirkirariyar fasahar AI, don cimma manufofi na soji.

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamhossein Darzi, ya yi gargadi game da amfani da fasahar ta (AI) da kuma amfani da ita wajen kara rura wutar yake-yake, musamman yake-yake biyu na Amurka da Isra’ila kan Iran a watan Yunin 2025 da Fabrairun 2026.

Da yake jawabi a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Darzi ya bayyana cewa saurin ci gaban fasaha yana canza yanayin yaki da da kuma asarar rayuka na fararen hula.

“Dole ne fasaha ta yi wa dan adam hidima kuma a yi amfani da ita kawai don dalilai na zaman lafiya, ba don zalunci, mamaye, ko keta hakkin mallakar kasa ba,” in ji shi.

Amfani da AI a matsayin kayan aiki don tayar da hankali da fadada rikici yana haifar da damuwa mai tsanani, musamman idan aka yi la’akari da rahotannin da ke bayyana yadda aka tura tsarin AI na zamani a lokacin harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.

Rahotanni sun bayyana cewa Amurka ta yi amfani da tsare-tsare na zamani a lokacin harin da ta kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu don yin nazari kan bayanan sirri, gano da fifita abubuwan da ake hari a kansu.

A ranar 11 ga Maris, 2026, kwamandan rundunar sojojin Amurka ta tsakiya (CENTCOM) ya tabbatar da amfani da kayan aikin AI na zamani a kan Iran, in ji Darzi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted