Wall Street Journal Ta Bayyana Cewa Donald Trump Ya Gajiya Wajen Bude Mashigar Ruwan Hurmuz

Jaridar “Wall Street Journal” ta Amurka ta buga wani labari da yake cewa; Shirin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya shelanta fara aiki da

Jaridar “Wall Street Journal” ta Amurka ta buga wani labari da yake cewa; Shirin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya shelanta fara aiki da shi na ” “yanci” a Mashigar ruwan Hurmuz, yana nuni da yadda karfin Washington yake da iya wajen sauya yanayin da ake da shi a daa daga cikin mashigar ruwa mafi muhimmanci a duniya.

Marubucin rahoton Gerard Martín y ace, dama tun da fari shelanta shiri irin wannan yana cike da hatsari,wacce Amurkan take tunanin kawo karshen ikon Iran akan mashigar ruwan.

Dama dai masana yankin mashigar ruwan Hurmuz sun sha bayyana cewa, babu wata kasa a duniyar nan wacce za ta iya kawo karshen ikon Iran akan mashigar ruwan ta Hurmuz.

Tun daga lokacin da Trump ya sanar da cewa Amurka za ta fara yi wa jiragen ruwa rakiya ta hanyar amfani da jiragen yaki saboda su ratsa ta mashigar ruwan Hurmuz, Iran ta bayyana cewa, ba wanda zai iya wucewa idan ba da izininta ba.

Yakin da Amurka da HKI su ka shelanta akan Iran na zalunci ne ya sa aka rufe mashigar ruwan ta Hurmuz, wacce kafin wancan lokacin tana a bude, ba tare da wata matsala ba.

Daga lokacin da ya shelanta yunkurin sojojin kasar tasa na bude mashigar ruwan na Hurmuz, zuwa dakatar da shi bai wuce, sa’o’i 48 ba.

Shugaban na kasar Amurka ya riya cewa ya dakatar da Shirin ne bisa bukatar kasar Pakistan da kuma wasu kasashe da bai ambaci sunayensu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted