Sُhugaban cocin Katolika Paparoma a Vatican ya bukaci a kawo karshen da gaggawa a Gaza sannan a gaggauta isar da kayakin agaji zuwa yankin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Paparoma Francis yana fadar haka a jiya Lahadi a likacinda yake jawabi kan bikin sallah mai tsarki a birnin Vatikan.
Paparoman ya kara da cewa yake yaken da ake yi a ko ina a duniya suna hana dawowar mai ceto. Ya kuma kara da cewa “Mun hana mai ceto dawowa tare da yake yaken da muke yi a duniya’. A wani bangare Paparoman ya bayyana cewa lokaci yayi na kawo karshen yaki a Ukraine da Gaza da sauran wurare a duniya. Ya bukaci HKI ta dakatar da yaki a gaza ta kuma bude hanyoyin kai agajin gaggawa ga Falasdinawa a yankin. Daga karshe paparoman yayi addu’a ta dawo da zaman lafiya a Gaza, Ukraine, Haiti , Sudan da sauransu.