Sojojin mamayan Isra’ila sun gudanar da rushe-rushen gidaje da gine-gine tare da kaddamar da samamen kama mutane a Yammacin Kogin Jordan
Sojojin mamayar Isra’ila sun gudanar da rushe-rushen gidaje da gine-gine na Falasdinawa a Khalil da Bait-Laham a ranar Talata, a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye. Sun kuma kama Falasdinawa 13 a lokacin hare-haren da suka kai kan yankuna da dama, yayin da a lokaci guda suka tumɓuke bishiyoyin zaitun da motocin bulldozer kusa da Ramallah.
Wakilin gidan talabijin na Al- Jazeera Mohammed Al-Atrash ya ruwaito cewa: Wasu motocin bulldozer na Isra’ila sun fara rushe wani gida na biyu a yankin Al-Dirat a gabashin Yatta, kudu da Khalil, bayan sun rushe wani gida mai fadin murabba’in mita 240 da Falasdinawa suka gina a shekara ta 2018.
Wakilin ya bayyana cewa: An rushe gidan farko ne da sunan an yi ginin ba tare da izini ba, ba tare da bai wa iyalan damar samun izini ko daukaka kara kan hukuncin ba.
Dan rahoton ya nuna cewa: Rushewar ta shafi kasancewar Falasdinawa a Yankin C, kamar yadda yarjejeniyar Oslo ta bayyana, wacce ta kunshi kusan kashi 62% na Yammacin Kogin Jordan.