Ministocin Harkokin Wajen ECO Sun Goyi Bayan Shirin Iran

Ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar ECO sun amince da shirin Iran na kawo karshen yakin Kasashen mambobin kungiyar hadin kan tattalin arziki (ECO),

Ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar ECO sun amince da shirin Iran na kawo karshen yakin

Kasashen mambobin kungiyar hadin kan tattalin arziki (ECO), a cikin wata sanarwa da suka fitar bayan wani taron majalisar ministoci a birnin Islamabad na Pakistan, sun bayyana goyon bayansu ga shirin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kaddamar kwanan nan don cimma mafita mai kyau da kuma kawo karshen yakin gaba daya da kuma har abada.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, wata sanarwa da aka fitar a taron majalisar ministocin Harkokin Wajen kasashen ECO a taron Islamabad a ranar Litinin ta bayyana goyon bayanta ga shirin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kaddamar kwanan nan don cimma mafita mai kyau da kuma kawo karshen yakin gaba daya da kuma har abada.

A cikin wannan sanarwar, kasashen mambobin ECO sun bayyana damuwarsu game da mawuyacin halin da ake ciki a yankin, suna jaddada muhimmancin kamewa, tattaunawa, da kokarin diflomasiyya, kuma sun bayyana goyon bayansu ga kokarin sulhu da Pakistan da Qatar suka yi.

A wani bangare na wannan sanarwar, kasashe mambobin kungiyar hadin kan tattalin arziki (ECO) sun bayyana damuwarsu game da yanayin tsaro a yankin (wanda ya samo asali daga harin soji na Amurka da ‘yan Sahayoniyya kan Iran). Sun bayyana goyon bayansu ga shirin Iran na kwanan nan na kawo karshen yakin da aka sanya gaba daya da kuma har abada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted