Najeriya Ta Nemi Sulhu Kan Rikicin Kakakin Ramaphosa A Kasar

najeriya ta nemi sulhu kan rikicinta da kakakin ramaphosa a kasar afrika ta kudu

Ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ya yi kira da a kai zuciya nesa tare da sulhu bayan kalaman da mai magana da yawun Shugaba Cyril Ramaphosa, Vincent Magwenya, ya yi game da Babban Jakadan Najeriya a kasar, Femi Fani-Kayode.

A wata sanarwa da ofishin ya fitar a shafinsa na X, ya jaddada cewa yana son a cigaba da wanzar da kyakkyawar alaƙar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Wannan takaddama ta samo asali ne bayan katsewar watsa shirye-shirye kai-tsaye a shafin YouTube na fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu, daidai lokacin da Fani-Kayode ke shirin mika takardun kama aikinsa ga Ramaphosa.

Bayan wannan katsewa, Fani-Kayode ya zargi jami’an da ke kula da watsa shirin da cire jawabinsa da gangan, sai dai ya yaba wa Ramaphosa bisa shiga tsakani da ya yi bayan an sanar da shi lamarin.

A martaninsa, Magwenya ya zargi Fani-Kayode da yin ƙarya game da shiga tsakanin da Ramaphosa ya yi a wannan matsala. Ofishin jakadancin Najeriya ya bayyana kalaman Magwenya a matsayin tsokana da rashin dacewa a tsarin diflomasiyya,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted