Iran Da Oman Sun Tattauna Kan Sabbin Yunkurin Diflomasiyya

Ministan Harkokin Wajen Oman ya bayyana cewa: Ya yi ganawa mai amfani da takwaransa na Iran kuma sun yi musayar ra’ayoyi kan sabbin yunƙurin diflomasiyya

Ministan Harkokin Wajen Oman ya bayyana cewa: Ya yi ganawa mai amfani da takwaransa na Iran kuma sun yi musayar ra’ayoyi kan sabbin yunƙurin diflomasiyya

Ministan harkokin wajen Kasar Oman Badr Al-Busaidi ya sanar da cewa ya yi wani taro mai amfani da Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, inda suka yi nazari kan yadda dangantakar kasashen biyu ta kasance, sannan suka tattauna matakan da za a dauka don zurfafa hadin gwiwa tsakanin Iran da masarautar Oman.

Al-Busaidi ya kara da cewa: Taron ya tabo batun kokarin diflomasiyya na warware kalubalen yankin, yana mai cewa shi da Araqchi sun jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa da tuntuban juna don rage tashin hankali da kuma cimma mafita cikin lumana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted