Asusun kula da kananan yara na MDD, (UNICEF), ya yi tur da hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan makarantu a jihar Kaduna dake tarayyar Najeriya.
Shugabar Asusun a Najeriya, Cristian Munduate, ta ce ya kamata kowane yaro dan Najeriya ya samu damar koyon ilimi cikin kwanciyar hankali.
A cewarta, ya zama dole a tabbatar wa dalibai da malamansu tsaro.