Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga harin da Ukraine ta kai wa jirgin ruwan kasuwanci na Iran a Tekun Caspian a lokacin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine.
Ya bayyana cewa ”Duk wani hari da aka kai wa ‘yan kasarmu ko muradunmu ba za a amince da shi ba, kuma dole ne a biya diyya”
Mista Araghchi ya ce, “takwaransa na Ukraine ya tabbatar masa ta wayar tarho cewa harin da aka kai wa jirgin ruwan Iran ba da gangan ba ne kuma Ukraine ba ta son wani tashin hankali.”
Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa, “Iran ba ta son tashin hankali, amma duk wani hari da aka kai wa ‘yan kasarta ko muradunmu ba za ta amince da shi ba kuma ”Dole ne a biya diyya ga asarar da aka yi.”
A cewar kamfanin dillancin labarai na IRNA, harin da sojojin Ukraine suka kai wa wani jirgin ‘yan kasuwa na Iran a Tekun Caspian da sanyin safiyar ranar Asabar data gabata, ya haifar da kakkausan martani na Tehran.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da harin na Ukraine, tana mai kiransa da cin zarafi, keta Dokar Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kara ta’azzara rashin tsaro, sannan ta jaddada ‘yancin Iran na kare muradun kasa da tsaronta.
An kuma kira babban jami’in harkokin wajen Ukraine a Tehran zuwa Ma’aikatar Harkokin Waje, kuma an isar masa da bacin ran Iran kan wannan mummunan aiki.