Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeskiyan ya ce a jawabin da ya gabatar a taron babban zauren MDD karo 81 ya fallasa Irin ta’asan da HKI da Amurka suka aikata a kasar Iran da yankin yammacin Asiya a yake yaken da suka farwa kasar da su a farkon wannan shekarar. Har’ila yau da kuma wadanda sojojin hayansu ‘yan ta’adda’ suka aikata a kan kasar Iran a cikin wannan lokacin.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkiyan na cewa: Amurka ta aikata ayyukan ta’addanci daban daban a wurare da dama a duniya, sannan ta horarda yan ta’adda wadanda suke masu aiki a wurare da dama a duniya.
Sannan HKI tare da goyon bayan Amurka sun aikata ayyukan ta’addanci suna kuma ci gaba da aikatawa a duk fadin duniya don cimma mummunan manufofinsu na ci gaba da babakere kan al-amuran duniya.
Shugaba yace maganar Trump a babban zauren MDD ta cewa zai shafe mutanen Iran miliyon 93 daga doron kasa ya sauka tunaninsa kan irin jawabin da yakamata a gabatar da gaban majalisar.
Yace a lokacinda muka haw kan mimbarin magana mun yi kokarin maida masa martani da kuma bayyanawa duniya hakikanin Amurka musamman wannan shu’umin shugaba Donal Trump.