Shugaban Majalisar Mulkin Sojin Sdan bayan rikicin hana shi bizar shiga Amurka ya bayyana cewa: Ba za su yi sulhu ba kuma ba za su yi wa kowa biyayya ba
A cikin jawabinsa na farko kan rikicin hana shi bizar shiga Amurka, Shugaban Majalisar Mulkin Soji ta Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana cewa: Sudan ba ta buƙatar biza daga kowace ƙasa. Ya yi watsi da abin da ya kira cin zarafi kuma ya jaddada cewa ƙasarsa za ta ci gaba da yaƙi ba tare da ja da baya ba.
Jawabin Burhan ya zo ne a lokacin ƙaddamar da shirin “Ba Mu Manta da Ku ba” don tallafawa ɓangaren lafiya. Da yake jawabi ga matasan Sudan, ya tabbatar da cewa ƙasarsa ba za ta miƙa wuya ga duk wani matsin lamba ko sulhu ba. Burhan ya ce, “Ba su son biza daga kowace ƙasa, ba su son kowa ya kashe musu kuɗi, ba su son komai. Za su zauna a cikin kasarsu tare da juna kuma zasu mutu a cikinta tare da al’ummar wannan ƙasar.”
A ranar 22 ga watan Satumban wannan shekara ta 2026, Amurka ta ƙi ba wa Burhan biza kafin jawabin da aka tsara zai gabatar a gaban Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan ya sa jakadan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya nemi Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani cikin gaggawa.