Jakadan Iran a MDD ya rubuta wasika ga babban sakataren MDD Antonio Goterres dangan da abinda babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO ta fadawa kwamitin tsaron na MDD dangane da bawa Amurka damar amfani da sansanonin sojojin kasashen Turai don kaiwa JMI hare hare.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya fadawa Gotress kan cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa musamman na MDD.
Gholam-Hossein Darzi, ya nakalto sakataren tsaro ta NATO yana fadar cewa, tun ranar 28 ga watan Fabrairu na wannan shekarar kasashen turai sun bawa jiragen yakin Amurka 500 damar tashi daga kasashen don kaiwa Iran hare hare.
Yace wannan zuwa watan Afrilui Kenan. Amma daga lokacin zuwa yanzun jiragen Amurka mai yuwa da na kasashen turai da dama sun kaiwa JMI hare hare, wadanda suka kasa kifar da gwamnatin kasar duk tare da baranin da suka yi mata.
Wasikar ta nuna irin goyon bayan da kasashen turai suka bawa Amurka a yake yaken da suka dorawa JMI. Da kuma rawqar da suka taka a yakin.
Ya ce a mahangar JMI bayanan babban sakataren NATO ya nuna irin yanda kasashen na turai suke da hannu dumudumu wajen zubar da jinin Iraniyawa a yake yaken da Amurka da HKI suka dorawa JMI. Tarayyar Turai da NATO suna da hannu a kissan Iraniyawa kuma wannan a binda ya bayyana Kenan.
Yace duk wannan ya sabawa doka ta 2/4 na MDD . Hari la yau ya sabawa dokokin kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa, saboda ya zuwa yanzun sun kasahe muatne fararen hula akalla 3,600 254 daga cikinsu yara kanana ne. sannan wasu 251 mata ne wadanda basa dauke da makami.
Wadannan shaidun sun tabbatar da cewa kasashen Turai suna tarayyar da HKI da Amurka a kissan kiyashin da suka aikata a irin a cikin shekaru 2025 da kuma 26. Wadannan suka suna cikin kudurin MDD mai lamba 33141(XXIX) wanda yake bayan me ake nufi da tsokana.