Ministan harkokin waje na kasar Iran Abbas Aragchi ya ce gwamnatin JMI ta bi dukkan hanyoyin diblomasiyya don tabbatar da cewa an bude mashigar ruwa ta Hurmuz amma bangaren Amurka ya ki amincewa da hakan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a jiya Asabar a babban zauren MDD a lokacinda yake magana da yan jaridu ya kuma kara da cewa, mafi yawan tattaunawan shugaban kasar Iran Dr Masuod Pezeshkiyan a gefen taron babban zauren MDD karo na 81 kan wannan batun ne.
Shugaban ya bayyana sharudda na bude mashigar ruwa ta Hurmuz. Ya ce shugaban ya gabatar da sharuddan da majalisar koli ta harkokin tsaron kasar Iran ta amince a matsayin sharadi na bude mashigar ruwa ta hurmuz.
Ya ce, shugaban kasar Amurka ya sabawa shawarar JMI, don haka a halin yanzu muna jiran amsa daga masu shiga tsakanin kasashen don sanin matakin da zasu dauka nan gaba.