Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi tir da kashe jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminaei(q) da iyalan gidansa wanda Amurka da HKI suka yi a ranar 28 ga watan Fabrayrun shekara 2026.
Kamfanin dillancin labaran Mehrnews ma kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a jawabin da ya gabatar a babban zauren MDD karo 81 abirnin NewsYork na kasar Amurka a jiya Asabar.
Lavrov ya zargi kasashen yamma da rikita al-amura a duniya, ta hanyar nuna fuska biyu a cikin al-amura da suke faruwa. Sannan ya sake jadda cewa kasar Rasha zata ci gaba da ;aikin soje na musamman da take yi a kasar Ukraine har zuwa karshe.
Lavrof ya ce: shugaba Putin ya bayyana cewa tsarin kama karya a duniya yana da matukar hatsari amma ya zama tarihi.