IRGC: Makaman Iran Zasu Fada Kan Jiragen Amurka A Tekun India

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC bangaren NAVY ko sojojin ruwa sun sun bada sanarwan cewa zasu kai hare

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC bangaren NAVY ko sojojin ruwa sun sun bada sanarwan cewa zasu kai hare hare kan jiragen ruwan Amurka a tekun India indan Amurka ta sake kawowa iran hare hare.

Ali Mohammadi  ya bayyana haka a jiya Asabar a birnin Bandar Abbas dake kudancin kasar. Ya kuma kara da cewa Iran ce take da cikekken iko kan mashigar ruwa ta Hurmuz, kuma wannan jawabin ya zo ne sakamakon kin amincewa da shawarorin da JMI ta bayar a MDD don kawo karshen rufe mashigar ruwa ta Hurmuz.

Kafin haka dai shugaban kasar Amurka ya sha yiwa Amurkawa da duniya karya kan cewa, mashigar ruwa ta Hurmuz a bude take, kuma jirage na wucewa ba tare da wata matsala ba.

Mashigar ruwa ta Hurmuz dai ta nan ne kasha 20 % na makamashi da kayakin sinadirai ayyukan noma suke fita zuwa kasashen duniya.

Muhamadi ya kara da cewa dukkan jiragen ruwa na daukan man fetur ko wasu kayaki tekun farisa, mashigar ruwa da Hurmuz tekun Omman da kuma tekun India suna karkashin kula da dakarun IRGC .

Kuma idan Amurka tana ganin ita ce ke kula da mashigar, to ta zo da jiragen yakin ta zuwa yankin.

Daga karshe muhamadi ya bayyana cewa, sojojina a shirye suke su kare kasar. Sannan zasu yi amfani da sabbin makamai da kuma sabbin dabardabaru don cimma manufofin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted