Mujallar Wall Street Journal ta watsa labarin cewa: Ma’aikatar Baitulmalin Amurkia ta bai wa ƙasashe zaɓi tsakanin fuskantar takunkumi ko kuma daina mu’amala da Iran
Mujallar Wall Street Journal ta bayyana cewa: Amurka ta ƙara matsin lamba ga abokan hulɗar cinikayyar Iran a cikin ‘yan makonnin nan, tana buƙatar ƙasashen Gabas ta Tsakiya da Turai su zaɓi tsakanin ci gaba da yin kasuwanci da Iran ko kuma ci gaba da hulɗar tattalin arziki da Amurka.
Mujallar ta ruwaito cewa: Wani babban jami’i a Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ya yi rangadi a ƙasashe da dama na yankin Gabas ta Tsakiya da Turai a wannan watan, yana isar da saƙon cewa ci gaba da ciniki da Iran zai iya wurga waɗannan ƙasashe da cibiyoyi ga fuskantar takunkumin Amurka.
Mujallar ta ambato Jonathan Burke, Mataimakin Sakataren Baitulmali kan Kudaden Tallafin ‘Yan Ta’adda, yana cewa: Amurka na Shirin daukan matakan gaggawa tsakanin abokan hulɗarta na magance buƙatun Amurka, yana mai lura da cewa yanzu suna ɗaukar matakan gabatar da gargaɗi mai muhimmanci.