Wani jami’an gwamnatin kasar Yemen ya bayyana cewa kwamitin tsaro na MDD ya rasa mutunsa da kuma matsayin da aka bashi na mai tabbatar da tsaro a duniya, saboda ya kasa tabbatar dazaman lafiya a Gaza haka ma ya kasa tabbatar da tsaron a kasar Yemen bayan da wasu kasashe suka mamaye ko suka take hakkin bil’adama a wadan nan yankuna.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Hizam Al-Asad wani jami’ii babban a cikin kungiyar Ansarullah yana fadar haka, ya kuma zargi kwamitin tsaro na MDD da gazawa, saboda ta kasa tabuka wani abu a kan abinda yake faruwa a Gaza da kuma yemen na kissan kiyashi da kuma take hakkin bil’adama.
Al-Asad ya kara da cewa kwamitin tsaron ya gaza tabuka wani abu na kawo karshen killacewar da saudia da kasashen yamma suka yiwa kasar yemen na tsawon shekaru 12 kuma a fili ya tabbatar da cewa kwamitin bai da wani abinda zata yi na kawo karshen matsalolin dan’adamtaka da suka bayyana ga kowa a duniya a Gaza, wanda HKI da Amurka suke jagorantar yin hakan.
Ya ce, zance ko maganar kwamitin tsaron bai da wani tasiri a kan manya manyan kasashen duniya da suke aikata abinda suka ga dama a wadan nan kasashen da ake zalunta aka kuma hana zaman lafiya a cikinsu.
Daga karshen yace kasar Yemen ta sha alwashin kwace hakkinta daga wadanda suka zalunceta ba tare da nuna gazawa ba.