Gwamnatin kasar Iran ta yi watsi da zancen shugaban kasar Amurka Donal Trump na kwace dukiyoyin Iran a matsayin ganiwar yaki, ta kuma bayyana cewa wannan zancen banzane wand aba zai kai shi ko ina ba. Sannan wannan zancen ya tabbatar da cewa shugaban yana yaki ne don cimma riba ko da kowa ta sha kaye a yakin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya bayyana haka ne a jiya Jumma’a a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka yana daukar abinda yake yi a Iran kwatankwacin abinda yayi a Venezuela ne. Inda ya kwace arzikin kasar daga hannun mutanen kasar.
Bakhaei ya bayyana cewa, ana samun ganimar yaki ne idan an sami nasara a kan mikiyi ne, amma nasarar da trump yake tunani yana cikin kwakwalwansa ne kawai, babu shi a kasa.