Trump Yace Amurka Da Iran Suna Ci Gaba Da Tattaunawa Don Kawo Karshen Yakin Da Ake yi

shugaban Amurka Donald trump ya sanar a jiya juma’a cewa lallai Amurka da iran suna ci gaba da tattaunawa domin ganin an kawo karshen yakin

shugaban Amurka Donald trump ya sanar a jiya juma’a cewa lallai Amurka da iran suna ci gaba da tattaunawa domin ganin an kawo karshen yakin da ake yi tsakaninsu, sai dai yace har yanzu Tehran baa shirye take ba a cimma wata matsaya.

Trump ya shaidawa yan jarida a fadar white hause cewa lallai tattaunawar dake gudana tsakaninsu da iran ya nuna cewa bangaren iran sun ba abin muhimmanci sosai fiye da lokutan baya, sai dai wannan baya nufi cewa dole a cimma matsaya ta karshe

Sai dai ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqci ya nuna cewa  Tehran bata fuskantar wata matsala da masu shiga tsakanin a tattaunawarsu da kasar Amurka , yace asalin matsalar itace tsarin da Amurka take amfani da shi da kuma yanayinta.

Yace lallai iran ta tabbatar da cewa ba za ta taba mika wuya ga girman kan Amurka ba, yace bama jin tsoron duk wata barazanar Amurka kuma ba za mu mika wuta ga duk wata matsin lamba ba, kuma ba zamu jurewa harshen barazana ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted