Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin yin gagarumin gyara a harkar kwallon ƙafa ta Nijeriya, bayan tawagar kwallon kasar ta kasa samun gurbin zuwa manyan gasa a matakin kasa da ƙasa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya Alhamis, Tinubu ya umarci Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC) da ta yi aiki tare da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta yadda ake tafiyar da kwallon kafa a kasar.
Gyaran zai mayar da hankali ne kan shugabanci da gudanar da kwallon ƙafa, wasannin cikin gida, bunkasa ’yan wasa da kuma tabbatar da daukar alhaki.
Tinubu ya ce Nijeriya na da hazikan ’yan wasan kwallon kafa da kuma goyon bayan jama’a, amma rashin tsarin gudanarwa ya hana kasar samun kyakkyawan sakamako.
Ya kuma umarci hukumomin kwallon ƙafa su tattauna da FIFA da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) yayin gudanar da gyaran, tare da tabbatar da cewa Nijeriya na bin ƙa’idojin kwallon kafa na duniya.