Shugaban kasar Iran mas’ud Pezeshkiyan a lokacin ganawarsa da firimiyan kasar Qatar ya bayyana masa cewa dole ne a amince da hakkokin alummar iran da doka ta basu, yace iran bata bukatar komai da wuce hakkinta karkashin doka, amma ba za ta mika wuya ga matsin lamba ko cin zarafi ba
Shugaban ya fadi wannan ne a lokacin ganawarsa da firimiyan kasar Qatar da ministan harkokin wajen kasar shaikh mohammad bin Abdurrahman al thani a ziyarar da suka kawo birnin Tehran a jiya alhamis, yace iran da Qatar kasashe biyu ne abokan juna kuma yan uwan juna duk da tashin tashina da ta faru a baya bayan nan
Pezeshkiyan ya kara da cewa kasashen amurka da isra’ila suna son lalata zaman lafiya da tsaro a yankin, ya ce yakin da suka kaddamar a baya bayan nan ya kawo cikas da jinkirin aiwatar da wasu yarjeniyoyi na hadin guiwa tsakanin iran da Qatar
Ana sa bangaren shaikh mohammad yace kasar Qatar tana son ganin an samu tabbaci da tsaro a yankin, kuma yana ganin yadda iran ke isar da sako ga kasashen dake makwabtaka da ita da kuma kokarin samun dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali