Isra’ila Tana Shirin Hana Falasdinawa Komawa Yankunansu

gwamnatin sahyuniya tana kokarin hana falasadinawa komawa gidajensu

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin HKI tana shirin hana dubban falasdinawa komawa gidajensu a sansanin yan gudun hjira guda 3 a arewacin gabar yammacin kogin jodan, inda suka jibge sojoji a yankunan kamar yadda rahotanni suka bayyana

Dakarun sojin Isra’ila sun shaidawa abin da suka kira da kotun kolin isra’ila cewa falasdinawa da suka tsere daga yankin Jenin, da tulkaran da nuru shams ba za a bari su koma gidajensu ba, saboda suna da kudurin ci gaba da kasancewa a yankunan domin yana da muhimmanci don kare  abin da ya bayyana da kula da tsaro.

Haka zalika isra’ila sun dauki matakin rushe rushe da gudanar da ayyuka a sansanonin, da suka hada da bude sabbin hanyoyi ga motocin sojoji, kuma wanan matakin yazo ne bayan tarwatsa falasdinawa dubu 10 daga sansanonin guda 3 lokacin da isra’ila ta kaddamar da yakin kare dangi a arewacin gabar yammacin kogin Jodan

hukumar kare hakkin bil adama ta human rights watch ta bayyana matakin isra’ila na tarwatsa falasdinawa daga gidajensu  da lalata kayayyakinsu a yammacin kojin jodan a matsayin cin zarafi da kuma keta dokokin kasa da kasa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted