Johson: Harin Da Amurka Ta Kai wa Iran Kuskure Ne Babba

tsohon jami'in birtaniya johson ya caccaki Amurka kan hari da ta kai wa iran

Tsohon fira ministan kasar Birtaniya Boris Johson ya fito fili ya soki Amurka game da matakin soji da ta dauka kan kasar iran, ya bayyana matakin a matsayin babban kuskure, kuma yace amurka ta fada cikin tarko saboda rashin dabara ko kuma wasu manufofi masu ma’ana.

Da yake Magana a wajen taron lokacin tattalin arziki na shuwagabannin duniya a birnin new delhi a jiya alhamis johson ya bayyana takaicinsa kan yadda amurka taki tuntubar babbar kawarta kafin ta kai hari kan kasar iran .

Yace da ta tuntubeta da ta taka muhimmiyar rawa wajen hana afkuwar yakin mara lissaf, yace tabbas da mun hanata fadawa  cikin wannan tarkon

Haka zalika tsohon jami’in ya caccaki matakin da jami’an tsaron birtaniya suka dauka inda ya tambayesu me yasa basu yiwa gwamnatin Washington gargadi ba game da mummunan tarkon da suke kokarin fadawa ba,  a matsayin  Amurka na babbar kawar birtaniya tana da hakkin samun cikakken bayani kan manufofin kai harin da kuma abin da zai biyo baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted