Kotun ICC Ta Ce Ba Zata Mika kai Ga Bukatun Amurka Ba

Shugaban kotun hukunta manya manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta bayyana cewa kotunta ba zata biyewa gwamnatin Amurka kan bukatunta na yin watsi

Shugaban kotun hukunta manya manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta bayyana cewa kotunta ba zata biyewa gwamnatin Amurka kan bukatunta na yin watsi da hukunta wadanda ake tuhuma da aikata manya manyan laifuka a duniya ba.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto mai sharia Tomoko Akane yar kasar Japan kuma shugaban kotun ta ICC na fadar haka a ranar Laraba, ta kuma kara da cewa ba zamu mika kai ga Amurka ba ko da ta kakabawa kotun kanta takunkuman tattalin arziki.

Mai sharia Akane ta kara da cewa bai kamata mu bar kotun ICC ta fadi ba. Don haka zamu yi duk abinda zamu iya don ganin wannan kotun ta ci gaba da ayyukanta.

Ta kuma kara da cewa, gaikiya ne akwai wasu kasashe masu rauni a duniya wadanda suka janye daga kotun, tare da umurnin Amurka. Tace mun fahinci irin halin da wadan nan kasashe a duniya suke ciki. Amma wannan ba zai taba kashe mana guiwa ba.

Ta ce bata adawa da wadannan kasashe saboda jenyewarsu daga kotun. Ta ce mu wata kotu ce wacce aka dorawa aikin binciken wadanda suka aikata munanan laifuka a duniya, wadanda suka hada da Benyamin Natanyahu firai ministan HKI da ministan yakinsa Yaof Galant.

Har’ila yau kotun ba zata dagawa gwamnatin Amurka kafa ba kan ta’asan da sojojinta suka aikata a kasar Afganistan na tsawon shekaru 20 da ta mamaye kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted