Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ce mosko za ta yi aiki tare da kasar iran wajen ganin sun tunkari sabbin takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa Iran da kuma cire matsin lambar takunkumin daga matakin kasa da kasa.
Da take mayar da martani a jiya game da takunkumin karya tattalin arziki da amurka ta sanya wa kasar iran Maria Zakhrova ta ce mosko za ta ci gaba da hadin guiwa da kasar Iran da sauran kasashe wajen ganin an kalubalanci matakin da ya sabama doka,
Haka zalika zakhrova ta kara da cewa an dade ana mayar da takunkumi zuwa kayan aiki na hukumta kasashen da basa goyon bayan kasashen yamma , tun da fari ma china tace takunkumin da aka sanyawa iran baya bisa ka’ida
Ana shi bangaren kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran yayi barazanar cewa Tehran za ta mayar da martani mai tsanani kan takunkumin Amurka, wajen daukar tsauraran matakai kan kasashen da suke ganin suna aiki da Washington