Gamayyar kasashen larabawa a MDD sun bada sanarwan cewa, ba za’a taba samun zaman lafiya a yammacin Asiya ba matukar HKI ta ci gaba da mamayar kasar Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday ta nakalto Alya Ahmed Al-Thani, jakadiyar kasar Qatar a MDD tana fadar haka da yawun dukkan kasashen larabawa a cikin Jamalisar, ta kuma kara da cewa akwai bukatar samar da adalci da kuma kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta a kan kasar Falasdinu wacce HKI ta mamaye. Idan ba haka ba ba za’a taba samun zaman lafiya a yankin yammacin Asiya ba.
Ta ce karuwan yawan kasashen da suke amincewa da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta, wani abu ne wanda dole sai an kai can. An bawa Falasdinawa yencin cin gashin kansu daga halin da suke ciki. Kuma wannan shi ne ya dace kasashen duniya su yi.
Wakiliyar kasashen Larabawan ta yi allawadai da HKI kan ci gaba da keta hurumin Falasdinawa da take yi a yankunan su da ta mamaye, da kuma kara yawan gine gine ga yahudawan da take yi a yakin yamma da kogin Jordan.
Riyad Mansour wakilin falasdinawa a MDD ya bayyana cewa HKI tana kokarin ganin ba’a samar da kasar Falasdinu mai zaman kanta ba. Hakama Ramiz Alakbarov wakilin MDD na musamman a yankin gabas ta tsakiya ya nuna damuwarsa da yanada HKI take ta ci gaba da keta yarjeniyar Gaza ta 10 ga watan oct. 2024.