Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya yi kira ga kasashen musulmi su hada kai a tsakaninsu don kawo karshen takalarsu da wasu kasashe suke yi.
Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Alhamis, a lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron hadin kai karo na 40 a nan tehran, ya kuma kara da cewa, Marigayi Imam Sayyid Aliyul Khaminaei (q) ya sha nanata muhimmancin hadin kai a tsakanin musulmi a duk fadin duniya. Don sai da hadin kai musulmi zasu sami daukaka da yenci da kuma gina kasashensu.
Yace duk tare da sabani da ke tsakanin musulmi hadin kai a tsakaninsu mai yuwa ne. Dangane da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran kuma shugaban ya bayyana cewa wannan kekyawar misali ne na ayyukan ta’addanci a kan kasashen musulmi, kuma tare da taimakon All..Iran ta tsaya ta kuma kare kanta daga daga ayyukan ta’addanci na wadan nan kasashe a kanta.
Ya ce Iran bata fara wannan yakin ba, kuma dole ne ta kare kanta daga makiya, amma ya kara tabbatar da cewa bai kamata wata musulmi ta bar makiya su yi amfani da kasarta don kaiwa wata kasa musulma hare ba.
Ya ce kasashen musulmi 57 a cikin kungiyar kasashen musulmi ta OIC, wadanda suke da jama’a kimani biliyon biyu a duniya, suke kuma da dimbin arziki, na kasuwanci, mata da kuma masana, zasu zama al-umma mai karfi a duniya idan sun hada kansu.
Daga karshen shugaban yace hadin kai tsakanin musulmi ba kauda bambancin ra’ayi a tsakaninsu ba, amma bai kamata ya maidasu makiyan juna ba.