Sharhi: Trump Ya Haramta ‘Palastine Action’

Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan shugaban kasar Amurka donal Trump ya shelanta masu gwagwarmaya a kasashen yamma musamman kasar Burtaniya wadanda ake

Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan shugaban kasar Amurka donal Trump ya shelanta masu gwagwarmaya a kasashen yamma musamman kasar Burtaniya wadanda ake kira ‘Palestine Action’ a matayin kungiyar yan ta’adda, wanda ni tahir amin zan karanta.

////…. Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya shelanta kungiyar ‘Palastine Action’ a matsayin kungiyar yan ta’adda, kamar yanda take daukar kungiyar Hamas a zirin Gaza na kasar Falasdinu da suka mamaye. Wannan matakin da gwamnatin trump ta dauka kan magoya bayana Falasdinawa a kasashen yamma, ya nuna cewa shuwagabannin wannan kungiyar, ba zasu taka kasar Amurka ba. Kuma dukkan dukiyoyinsu da suke kasar Amurka za’a kwacesu.

Gwamnatin kasar Amurka a yau ta na daukar wannan kungiyar wacce ta samo asali daga kasar Ingila ta fara yaduwa zuwa kasashen yamma da dama, daga ciki har da kasar Amurka. Kungiyar Palastine Action ta bulla ne bayan fara yakin tufanul aksa a Gaza a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2020. Sannan ta kara karfi a lokacinda HKI ta fara kissan kiyashi a gaza, wanda ya zuwa yanzu sun kashe falasdinawa fiye da dubu 73.

Kuma sun daidai da yankin na Gaza da kasa. Miliyoyin Falasdinwa suna rayuwa a cikin rumfunan da basu kai wanda ya dace a kwana acikinsa ba. Amma basu da zabi.

Trump yana zargin kungiyar Palastine Action da yada tunaninta , na abinda ta kira ayyukan ta’addanci, a wasu kasashen wanda ya hada da kasar Amurka. Shugaban yace, daga yanzu shuwagabannin wannan kungiyar bazasu shiga kasar Amurka ba a duk tsawon rayuwarsu. Haka duka wata dukiya ko kadara na kungiyar wadanda suka hada da asusun bankunan yayan kungiyar duk za’a rufe su. Banda haka yace Amurka zata hana dukkan kamfanonin fina finan Amurka aiki da su.

Hakama za’a yanke kungiyar daga amfani da tsarin bai daya na kudaden duniya. Banda haka haramcin zai hana kowa bawa yayan wannan kungiyar kudade ko wani abu ko menen karancinsa.

Bayanin ya kara da cewa yan kasar Burtania wanda suke fita zanga zanga tare da yayan wannan kungiyar, su ma zasu fuskanci makoma guda.

Richard Barnard da kuma Huda Ammori ne suka kafa harsashin kafuwar kungiyar a cikin watan yulin shekara ta 2020.

A kasar Burtaniya dai gwamnatin kasar ta sanya kungiyar cikin kungiyoyin yan ta’adda ne a lokacinda suka kai hare hare kan sansanin sojojin saman ‘ stormed RAF Brize Norton’ suka kuma bata wasu jiragen yaki tare da watsa penti a cikin injunansu.

Marco Rubio sakataren harkokin wajen Amurka, wanda ya bada sanarwan haramcin ya bayyana cewa kungiyar ‘Palastine Action’ ta zama barazana ga zaman lafiya a kasashen yamma musamman Amurka.

Ya ce kasashen yamma zasu yi amfani da dukkan hanyoyin da suka gay a dace na yaki da ayyukan ta’addanci, zamu yaki duk wanda yake son ya sauya rayuwarmu a kasashen yamma, inji shi.

Shi ma sakataren kudi na Amurka Scott Bessent ya ce zasu zo da dukkan hanyoyin takurawa ta tattalin arziki don murkushe yan ta’adda a kasashen yamma. Yace yan ta’adda na siyasa basu da wuri a kasashen yamma, kuma ba za’a barsu su nummafasa ba.

A wasu bayanin, an nuna cewa Palastine Actoin sun fara lalata dukiyoyin kamfanoni masu zaman kansu da kuma na gwamnatine bayan yakin 7 ga watan Octoban shekara 2023. Inda suka kaiwa kamfanin Elbit ta makamai ta HKI a kasar Burtaniya, suka kuma jawo masa asarar fam miliyon 1.2 a shekara 2024.

Sannan a cikin watan Yuni na wannan shekara wata kotun daukaka kara a Burtania ta yanke hukuncin tabbatar da matakin haramta kungiyar wanda gwamnatin kasar Burtaniya ta yi. Kotun ta ki amincewa kungiyar ta bayyana albarkacin baki ne kawai ba. Sai dai wadanda suka assasa kungiyar har yanzun suna da damar daukaka kara zuwa kotun kolin kasar.

A lokacinda yake maida martani kan matsakin da shugaba Trump ya dauka a kan kungiyar, Ms Ammori daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar ta fada a shafinta na X, Trump ya shelanta kungiyarsa a matsayin kungiyar yan ta’adda, wannan ya nuna cewa, iata da ta kasance ba falasdinaya ce daga kasar sannan yar kasar Iraki, Trump yana adawa da duk abinda yake da dangantaka da Falasdinu ne kawai. Kuma shi ne ya wargaza dukkan kasashe ne guda biyu. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted